Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa matsalar tsaro da ake fama shi a kasar nan nuni ne cewa akwai shirgegen baraka a gwamnati musamman game da tsaro.
Mahara dauke da muggan makamai sun far wa fitaccen gidan shakatawa dake garin Kajuru da ake kira ‘Kajuru Castle’ inda suka kashe Faye ‘yar kasar Britaniya da wasu mutane uku.
Maharan sun far wa wannan gida ne da misalin karfe 11:30 na safe ranar Juma’a.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna Yakubu Sabo ya bayyana cewa maharan sun farwa wannan gida ne a daidai wasu masu yawon bude ido suna shakatawa a wannan gida.
Bayan wadanda aka kashe maharan sun yi garkuwa da wasu da dama.
” Faye ta zo wannan gida ne a Kajuru da yakinin cewa za a samar mata da tsaro amma hakan bai samu ba.
Ana ta yayadawa cewa babu matsalar tsaro a jihar. Gashi hakan ya sa wasu sun rasa rayukan su babu gaira babu dalili. Dama can ana ta yin farfagandan karya ce cewa an shawo kan matsalolin rashin tsaro a jihar bayan kuwa abin dada gaba yake yi musamman a wannan yanki na Kajuru.
” Dole ne gwamnatin tarayya ta biya ‘yan uwan Faye diyyar ran ‘yar uwan su da aka kashe a garin Kajuru.
Sannan kuma sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin Tarayya da ta kara maida hankali wajen samar da tsaro a musamman yankin Arewa Maso Yammacin kasar nan da kasa baki daya.
” Muddun ka ga ana samun matsaloli irin haka musamman wanda ya shafi tsaro da ya ki ci yaki cinyewa, to ko gwamnati ta gaza ko kuma kasar ce gaba daya ta dauko hanyar rugujewa. Domin kuwa abin ya dade yana ta tangal-tangal a kasa.
