Mazauna Abuja ’yan asalin Jihar Katsina sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda su ka yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta dakatar da kisan-gillar da ake yi wa al’ummar jihar Zamfara tare da yawan garkuwa da su.
Sun gudanar da zanga-zangar a jiya Asabar a Abuja, tare da nuna bacin rai ganin yadda matsalar tsaro ke ta kara tabarbacewa ta hanyar yawaitar kashe-kashe-, garkuwa da mutane da kuma kona gidaje da dukiyoyi.
Wata da ke cikin wadanda suka shirya taron zanga-zangar, mai suna Fatimah Mustapha, ta ce sun fito ne domin yin kira ga gwamnati ta fa san cewa ana ci gaba da yi wa jama’a kisan gilla da yawaitar garkuwa da mutane a Zamfara.
Fatima ta ce masu yin wannan ta’addanci a kullum sai ma kara fitowa fili su ke yi su na aiwatar da kisa da garkuwa, kan su tsaye.
Ba tare da ana daukar wani matakin gaggawa na kawo karshen fitinar ba.
Ta ci gaba da cewa gwamnatin Jihar Zamfara ba za ta iya shawo kan fitinar ba, dalili kenan su ka yanke shawarar yi wa Buhari zanga-zanga a Abuja, fadar gwamnatin tarayya.
Fitacciyar tsohuwar ‘yan jarida, Kadaria Ahmed, wadda ta na daya daga cikin masu shirya zanga-zangar, ta roki Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro su kara kaimi wajen dakile matsalar rashin tsaro a Zamfara.
“Shugabannin mu sun ma daina magana a kan wannan mummunar matsala ta kashe-kashe. Wannan kuwa abin haushi da takaici ne matuka.
Abu ne da ya shafi asarar rayuka.
Kare rayukan jama’a ya kamata gwamnati ta yi.”
Shi kuwa wani tsohon hadimin gwamna Abdul’aziz Yari, mai suna Zagaraddeen Bello-Imam, ya roki gwamnatin tarayya ta dauki kwakkwaran matakin a-yi-ta-ta-kare domin a samu zaman lafiya a Jihar Zamfara.
Sannan kuma ya yi kira ga Buhari da ya yi garambawul ga shugabannin tsaron kasar nan.
Masu zanga-zangar sun tashi daga Unity Fountain har suka dangana da Kofar Fadar Shugaban Kasa, inda suka kai kukan su.
Mai Taimakawa Na Musamman Ga Shugaban Kasa a Harkokin Tsaro, Usman Ibrahim, ya yi alkawarin isar da sakon su ga shugaba Buhari.
Discussion about this post