Akalla mutane 22 aka bada rahoton mutuwar su, sanadiyyar wani sabon rikici da ya barke a tsakanin kabilun Tivi da Jukun, cikin Karamar Hukumar Wukari, Kudancin Jihar Taraba.
Makonni uku kenan wadannan kabilu biyu su na fada a tsakanin su, ana kashe juna tare da barnata dukiyoyi.
Wani ganau ya ce mahara ‘yan kabilar Tivi ne suka dira wata unguwa da ke gefen Wukari, da karfe 7 na safiya.
Bwacha David ya ce maharan sun haura 200, wadanda suka dira kauyen ba tare da shirin mazauna kauyen ba.
Ya ce sun rika banka wa gidaje wuta, kuma suka kashe sama da mutane 10.
Shugaban Karamar Hukumar Wukari, Adi Daniel, ya tabbatar da kai harin, ya ce gaskiya ne an kai hari a Wukari.
“A gaskiya an fa fara kai mu makura. Mu ma za mu kai ga fata daukar fansa, tunda abin na su ya wuce gona da iri.
‘Wannan ne karo na takwas da kabilun Tivi suka kawo mana hari kwanan nan. Sun kashe mana sama da mutane 22, mu kuma ba mu kashe musu ko kwaro daya ba.
“To kuma harin da suka kawo yau, sun yi shi bayan zaman sulhun da aka yi ranar Litinin.” Haka Daniel ya ce.
Sai dai shi kuma shugaban kabilar Tivi, Orbee Uchiv, ya ce Jukunawa ne suka fara kai musu hari.
Ya ce ranar Litinin Mataimakin Gwamnan Taraba da na Benuwai sun hadu da Aku Uka na Jukun da Tor Tiv na kabilar Tivi, inda suka yin kira a zauna lafiya.
“Amma da safiyar Talata sai aka kai wa Vaase hari, aka kashe sama da mutane bakwai.
Ranar Laraba an banka wa kauyen Tse Kaakigh wuta gaba dayan sa.
Kakakin ‘Yan sanda David Misal ya tabbatar da harin.