KARIN ALBASHI: Irin godiyar da na ke so ma’aikata su yi – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya hori ma’aikata su kara jajircewa da kuma maida himma wajen aiki, sakamakon karin albashi da aka yi.

Ya kuma yi kira ga Kungiyar Kwadago ta Kasa, ta nuna nuna dattako wajen yin la’akari da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ci.

Buhari ya yi wannan tsokaci ne a jiya Alhamisa a lokacin da ya ke sa hannu wajen karin mafi kankantar albashi, daga naira 18,000 zuwa naira 30,000.

Ya ce “Ina son ganin a kowane matakin albashi ma’aikaci ya ke, to ya kasance ya kara himma wajen kuda da aikin sa.

“Ina kuma so Kungiyar Kwadago ta yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki. Ga yawan al’umma, ga bukatun gyaran hanyoyi, asibitoci da sauran fannoni da yawa.

“Saboda haka ina yi wa ma’aikatan Najeriya fatan alheri.” Inji Buhari.

Shi kuma Ita Enang, Mashawarcin Shugaba Buhari a Harkokin Majalisar Dattawa, ya ce wannan tsari ya fara ne tun daga jiya Alhamis, 18 Ga Nuwamba, 2019.

Saboda haka ana bada sanarwar za a fara amfani da wannan tsari wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kan su da wannan sabon tsari daya albashin watan Afrilu.

Ya ce wannan sabon tsari ya zama dole a yi amani da shi, tunda ya zama doka.

Enang ya ce wannan tsari “bai shafi duk wani wanda ma’aikatan da ke aiki a karkashin sa ba su kai 25 ba.

Akwai kuma wadanda ke aiki a jiragen ruwa masu lulawa su

Wasu yankunan da inda ya ke aikin ba. Sai kuma ma’aikatan da ke aiki a karkashin wata yarjejeniyar da aka cimma da shi tun kafin ya fara aikin.

Sannan kuma ya ce doka ta ba ma’aikaci damar ya maka wanda ya ke wa aiki kotu idan ya ki biyan sa sabon tsarin albashin.

Doka kuma ta ba Minsitan Kwadago ko wani da ya wakilta damar maka wanda ya i biyan sabon tsarin zuwa kotu domin a nemar wa wadanda ya tauye hakkin su.

Ya ce Hukumar Kula da Tsarin Albashi da Ma’ikatar Kwadago ce za su tabbatar da ana bin wannan sabon tsari.

Wannan dokar ta shafi kowa, kowane kamfani da ma’aikatu na Najeriya.

Share.

game da Author