KARAMAR MAGANA TA ZAMA BABBA: Ali Nuhu ya maka Adam Zango a Kotu

0

Bayan bidiyon da Adam Zango ya fitar da yake zargin Jarumi Ali Nuhu da yin birus ga yaran sa dake ci masa mutunci a farfajiyar fina-finan Hausa sannan kuma shi Ali da kansa baya iya cewa Komai wannan zargi ya zama babban magana.

Zango ya bayyana cewa Ali Nuhu ya gagara hana yaran sa ci masa mtunci da suke hada wa da mahaifiyar sa. Yace ba zai iya hakuri ba muddum aka zagi mahaifiyarsa.

Ali Nuhu bai ce komai ba tun bayan da Zango ya saki wannan bidiyo, kwasam sai a ranar Alhamis Zango ya ga sammaci daga Kotu cewa Ali ya doka shi yana neman ya bayyana domin wanke kan sa bisa zargin cin fuska da yayi masa da kazafi.

Kotu na bukatan Zango ya bayyana a gabanta ranar 15 ga watan Afrilu domin amsa wasu tambayoyi da ak ce ya fadi game da Ali Nuhu.

Wannan shine kusan karo na farko da ‘yan wasan fina-finan Hausa zasu kai dayan su kotu bisa wani korafi ko zargi.

Abin dai bai yi wa da dama daga cikin abokanan aikin su dadi ba.

Da dama suna ganin, Ali Nuhu ya yi hakuri da Adam Zango sosai domin tunda hayaniya ta shiga tsakanin su Ali Nuhu bai taba fitowa fili ya soki Zango ba ko kuma yayi wani magana game da shi ba. A mafiyawan lokutta ma Zango ne kan sanar da mutane cewa shi da Ali ba su zaman lafiya.

Bayan amsan sammancin Zango ya rubuta a shafin sa ta Instagram cewa ” ALHAMDULILLAH ALLAH YASA MU DACE! ALLAH YASA MUNA DA TSAWON RAI. NA BAYAR DA RAINA FANSA AKAN MUTUNCIN UWATA DA MUTUNCINA KUMA BAZAN TABA YIN DANA SANI BA KO MENENE ZAI FARU DANI.”

Share.

game da Author