Zababbun ’Yan Majalisar Dokoki 14 na PDP sun kaurace wa karbar satifiket daga hannun INEC, wanda aka gudanar jiya Laraba ga wadanda suka yi nasara a zaben 2019 a jihar.
INEC ta bayar da satikfiket ga zababben gwamna, Abdullahi Ganduje, Mataimakin sa da sauran Mambobin Majalisar Dokokin Jihar na jam’iyyar APC.
A jawabi da Kakakin Yada Labarai na dan takarar gwamnan Kano na PDP, Abba Yusuf, ya ce an umarci zababbun da su kaurace saboda dalilai na tsaro.
Ya ce jam’iyyar PDP ba ta gamsu da wurin da aka kebe domin gudanar da bikin mika satifiket din ba.
“Mambobin PDP ba su gamsu da yanayin tsaro a Cibiyar Wasanni ta Sani Abacha ba, da ke Kofar Mata ba.
“PDP ta rubuta wa INEC wasika cewa ta na son a canja wuri, inda kowane bangare na jam’iyyu za su ji cewa ba su fuskantar barazana ga rayuwar su, kamar yadda aka yi a 2011 da 2015.
“Daga nan sai muka umarci mambobin mu da kada su halarci bikin, har sai mun ji daga INEC dangane da amsar da za ta ba mu tukunna.
“Amma abin haushi da bakin ciki, INEC ta maida kan ta a Kano tamkar wani bangare na gwamnatin Kano, ko kuma wani reshe na jam’iyyar APC.”
Shugaban INEC na Kano, Katsina da Jigawa, Abubakar Nahuce, ya roki masu mukamai da a tunkari ayyuka kuma a daina siyasar ko a ci ko a mutu.