KANJAMAU: Tsadar maganin PrEP ne ya sa gwamnati ba ta iya wadata shi a asibitocin kasar nan – Sani Aliyu

0

Wata mai sana’ar Karuwanci dake zama a unguwar Kubwa a Abuja mai suna Joan ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a duk tsawon shekarun data tayi tana sana’ar karuwanci ba ta taba sanin cewa akwai maganin da zai kare mutum daga kamuwa da cutar Kanjamau mai suna Pre-Exposure Prophylaxis (PrEP) ba.

Joan ta ce takan kwana da maza da dama a kullum amm kororo roba take amfani da shi ko kuma namijin dake kwana da ita domin kare kan su.

Ita ma Gloria mai shekaru 26 dake iri wannan sana’a ta ce bata taba sanin cewa akwai irin wann magani ba. Ita ma dai cewa tayi da kororo roba take kare kanta.

Daga nan wakiliyar PREMIUM TIMES ta ziyarci wasu asibitocin gwamnati dake Abuja duk asibitocin sun tabbatar mata cewa basu da maganin PrEP.

Wata ma’aikaciyar asibitin Kubwa ta bayyana cewa asibitin kan bada wannan magani kyauta amma idan suna da shi. Tace samun maganin na basu wahalar gaske.

Wata killa za a iya samun wannan magani a asibitocin dake zaman kansu ko kuma a asibitin kula da masu kanjamau amma fa da tsada.

Suma asibitocin dake zaman kansu sun bayyana cewa da kyar suke samun maganin sannan koda sun samu akwai dan karan tsada.

A hiran da suka yi shugaban hukumar (NACA) Sani Aliyu ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya ba za ta iya samar da wannan maganin ba saboda tsadar da yake da shi.

” A lisaffe maganin PrEP da mutum daya zai sha na wata daya ya kai Naira 468,000. Yace gwamnati bata da irin wadannan kudade domin samar da wannan magani.

Share.

game da Author