A taron wayar da kan mutane game da illolin zazzabin cizon sauro da aka yi a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja kamfanin sarrafa magani dake kasar Korea ‘Shin Poong’ ta kaddamar da sabuwar maganin kawar da zazzabin cizon sauro mai suna ‘Pyramax’.
Da yake ganawa da manema labarai shugaban kamfani Wonjune Chang ya ce kamfanin su ta yi haka ne domin tallafa wa gwamnatin Najeriya wajen dakile yaduwar cutar.
Wonjune ya ce kamfanin su ta hada hannu da kamfanin sarrafa magunguna a Najeriya mai suna ‘Dovizia Pharmaceutical Services’ domin tallatar da maganin a duk fadin kasar nan.
“Mun sami karfin gwiwar kaddamar da wannan magani a kasar nan ne bayan tabbatar da da ingancin maganin daga gwamnatocin kasashen duniya da hukumomin tantance ingancin magaunguna.
Bayan haka jami’in ‘Dovizia Pharmaceutical Services’ Oladipupo Ojo ya ce kamfanin Shin Poong ta yi amfani da sinadarori masu inganci wajen sarrafa maganin domin ganin cewa maganin ya kashe kwayoyin zazzabin cizon sauro a jikin mutum ba tare da matsala ba.
“Pyramax na da ingancin kashe kwayoyin zazzabin cizon sauro a jikin mutum ba tare da ya sa laulayi ba a jikin mutum. Sannan za a iya samun saukin ciwon a cikin awowi kalilan bayan an sha magani.
A karshe ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya jinjina wa kokarin da kamfanin Shin Poong ta yi wajen ganin an kawar da zazzabin cizon sauro a kasar nan.
Ya kuma ce gwamnati za ta ci gaba da mara wa duk kamfanin da ta bada gudunmawarta a yaki da zazzabin cizon sauro a kasan.
Hanyoyin guje wa kamuwa da zazzabin cizon sauro.
1. Tsaftace muhalli.
2. Nome duk ciyawa dake ciki da wajen gida.
3. Kwana cikin gidan sauro.
4. Zuwa asibiti domin gwajin cutar da zaran an kamu da zazzabi.
5. Shan maganin zazzabin cizon sauro yadda ya kamata.
6. A daina barin ruwan da za a yi amfani da shi a gida a bude domin haka na zama makwancin sauro.
7. Yin amfani da maganin sauro.
8. Saka raga a kofofi da windunan gida domin hana sauro shigowa gida.
Discussion about this post