Jami’in rundunar ‘yan sandan jihar Legas Christian Madza ya bayyana cewa jirgin kasa ya markade mutane hudu dake tafiya a cikin babur din keke NAPEP.
Madza yace wannan abin tashin hankali ya faru ranar Talata a mahadar titin mota da hanyar jirgin kasa dake Iju-Fagba.
Ya ce wadannan mutane sun gamu da ajalin su ne a daidai suna kokarin tsallaka mahadar titi da hanyar jirgin da direban keke NAPEP ya nemi yi yayin da jirgin ke dosowa.
Madza yace a dalilin haka kuwa mutane hudu suka mutu nan take sannan daya ya sami rauni.
Ya yi kira ga mutane da masu ababen hawa da su rika kula wajen bi ta kan titin jirgin don gujewa irin haka. Sannan kuma ya ce an saka tambari manya a hanyoyi da titunan domin yi wa duk wani da ya doso inkiya da ya kula da kuma yin taka tsantsan a hanyar.