Jaridun Najeriya na bukatar yi wa kan su tarnaki da dabaibayi -Osinbajo

0

Babban Mai Taimakawa Ga Mataimakin Shugaban Kasa A Yada Labarai, Laolu Akande, ya bayyana cewa idan kafafen yada labarai na Najeriya suka kafa wa kan su da kan su ka’idoji, sharudda, hakan zai iya kawar da dokokin da gwamnati ke gindaya musu.

Akande ya yi wannan bayani ne a wurin taron karin sani a kan “Ka’idojin Da Shari’a Ta Gidaya Kan Sha’anin Bincike A Aikin Jarida’, jiya Litinin a Abuja.

Taron dai na kwana biyu ne, kuma jaridar Daily Trust ce ta shirya shi tare da hadin guiwar Cibiyar Dabbaka Ka’idojin Shari’a a Matakan Aikin Jarida, wato, Center for Media Law and Development.

Akande ya wakilci Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ne a wurin taron, inda kuma ya kara da cewa kafa sharudda, ka’idoji da dokoki tare da famimtar hurumin dokar aikin jarida, zai kara wa kafar yada labarai kima, kwarjini da martaba.

Hakan kuma inji Akande zai iya kauce wa daga buga labarai na bogi tare da samar da yanayi na inganta bincike a kafafen yada labarai.

Ya ce samuwar soshiyal midiya a duniya ya kara samar da kafa ko kafofin yada labarai na bogi da marasa tushe balle makama, su na ta watsuwa kamar wutar-daji, tare da cusa wa masu karatu mummunar fahimtar wani abu wanda ba hakan ya ke ba.

Akande ya buga misalai da dama, musamman inda ya yi dogon bayani dangane da yadda aka rika yada labaran bogi a lokacin kamfen da zaben 2019.

Shi ma babban lauya Femi Falana, cewa ya yi tsarin binciken labarai abu ne mai hatsarin gaske, don haka akwai matukar bukatar a samar wa tsarin dokar da za ta kare shi tare kuma da yi wa tsarin kandagarki.

Mawallafin PREMIUM TIMES, Dapo Olorunyomi kuwa, cewa ya yi tsarin binciken labarai abu ne mai wahalar gaske, kuma mai bukatar gaskiya da amanab tare da tabbatar da cewa ba a saki layin kima da darajar gidan jarida ba.

Dapo wanda shi ma ya gabatar da takarda a kan tsarin binciken kwakwaf, ya kara da cewa matsawar aka saki layi, ko karbar wata kyauta ko toshiyar baki zai iya zubar da kima da darajar gidan jarida.

Share.

game da Author