Wani jami’in tsaro ya kutsa da mota cikin taro jerin gwanon masu bikin Easter, har ya kashe mutane takwas a ranar Lahadi da dare.
Ganin haka, sauran wadanda suka tsira da ran su sai suka hau mai motar da kuma daya fasinja da suke tare da duka, su ka yi musu lilis, har suka kashe su.
Al’amarin ya faru a daidai mahadar hanyar Alheri, kan titin Biu, a Jihar Gombe.
An ce direban motar jami’in tsaro ne na hukumar NSCDC, shi kuma abokin tafiyar sa a motar, wanda kuma aka kashe su tare, dan sanda ne.
Wani babban jami’in Boys Brigade mai suna Isaac Kwadang a jihar Gombe, ya shaida wa ‘yan jarida cewa sun samu labarin al’amarin wajen karfe 11:30 na dare ac ranar Lahadi.
Ya ce jami’in tsaron wanda ba kan aiki ya ke ba, ya hadu da masu jerin gwanon a kan titi, sai suka fara sa-in-sa da matasan da ke cikin jerin. Daga nan sai ya yi gaba.
An ce ya ja da baya, ya kashe fitilar motar sa, sannan ya sa giya ya darkaki cikin gungun masu jerin gwanon, inda a nan take ya kashe mutane takwas.
Yawancin wadanda suka mutu mambobi ne na Boys Brigade.
Daga nan sai matasa suka cim ma direban da abokin tafiyar sa, nan da nan suka rufe su da duka har suka mutu.
Shi ma Shugaban Asibitin Kwararru na Jihar Gombe, Shu’aibu Muazu, ya ce an kai wasu gawarwaki asibitin na sa.
Discussion about this post