Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magungunan ta kasa (NAFDAC) ta yi kira ga mutane da ma’aikatan kiwon lafiyar kasar nan da a maida hankali sannan a kula matuka domin akwai magungunan Kwalara na jabu da ya karade kasuwannin kasar nan da ake kira ‘Dukoral’
Shugaban hukumar Moji Adeyeye ce ta yi wannan kira ranar Litini a Abuja inda ta kara da cewa maganin ya bazu a kasuwannin kasar Bangladesh.
Adeyeye ta ce NAFDAC ta sami tabbacin haka ne daga Kungiyar kiwon lafiya ta duniya dake kasar Bangladeshi (WHO) bayan ta gudanar da bincike kan ingancin wannan magani.
” Shi dai wannan magani na dauke da rubutun harsunan Turanci da Faransanci sannan kamfanin sarrafa magunguna na Valneva Canada Inc. ce ta sarrafa maganin amma bincike ya tabbatar mana cewa kamfanin Valneva Canada Inc. ba ita bace ta sarrafa wannan magani.
” A dalilin haka muke kira ga duk masu shigo da magugunan daga kasashen wajen kan su sa ido matuka.
Adeyeye ta kuma ce mutane da ma’aikatan kiwon lafiya za su iya tuntubar ofishin hukumar mafi kusa da su domin sanar da hukumar idan aka yi kicibis da wannan jabun magani.