Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya yi kira ga iyaye da dalibai ‘yan Najeriya dake ke so suyi karatun likitancin a jami’o’in dake kasar Ukraine da su binciki kwarewar makarantar da shaidar amincewa da digirin su kafin su tafi.
Adewole ya yi wannan kira ga iyaye ne a ranar Talata bayan sauraron kalaman da mininstan kiwon lafiya na kasar Ukraine ya yi cewa bashi da tabbacin ingancin ilimin da wasu jami’un dake gabashin kasashen Turai ke koyarwa ba.
” Ministan ya bayyana cewa ma’aikatar kiwon lafiyar kasar Ukraine bata da tabbacin ingancin ilimin da jami’ar Odessa National Medical University ke badawa
Adewole yace a dalilin haka ne yake kira ga iyaye da dalibai da su yi bincike kafin su tura ‘ya’ayn su can.