INEC ta karyata Atiku a kotu

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta zargi dan takarar shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da kirkirar wa kan sa sakamakon zabe na karya, domin kafa hujja da shi a gaban Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa na 2019.

Wannan ya na daga cikin martanin da INEC ta yi wa Atiku a kotun, inda ta ce babu wani rumbu na na’ura da INEC din ta tattara sakamakon zaben 2019 ballantana har Atiku ya yi ikirarin ganin abin da ke ciki har ya kwafo ya nuna.

An yi ta sa-toka-sa-katsi a kan wannan ikirari na Atiku, har jami’an tsaro suka fara binciken yadda Atiku ya yi ya gano sakamakon da ya yi ikirari.

Lauyan INEC, Yunus Usman (SAN), ya bayyana cewa ko kusa ba a tattara sakamakon zaben shugaban kasa ko watsa shi a na’urorin sadarwa ba.

INEC ta kara da cewa babu wani rumbun na’urar da ta tattara ko ta killace sakamakon zaben 2019 a ciki, ballantana har a ce Atiku ya shiga ya leko sakamakon zaben da ya yi ikirarin cewa shi ya samu.

Atiku ya yi ikirarin cewa kuri’u 18,356,732 ya samu, shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya samu 16,741,430.

Atiku ya ce ya yi nasara a kan APC da kuri’u 1,615,302. Sai dai kuma INEC ta ce wannan duk shaci-fadi ne da zuki-ta-malle, amma babu inda INEC ta killace sakamakon nzabe a na’urar zamani da har Atiku ya shiga ya dubu, ko wani ya shiga ya dubo masa.

Darakan Yada Labarai da Fasahar Zamani na INEC, Chidi Nwafor ne maimaita haka a cikin bayanin da INEC ta tura wa kotu a rubuce cewa zargin da Atiku ya yi ba gaskiya ba ne.

Ya ce Buhari ya yi nasara ne bisa zaben sa da aka yi, amma babu wani sakamako na daban, wanda Atiku ya yi ikirarin cewa sakamakon wai ya nuna shi ne ya yi nasara.

Nwafor yace iyakar adadin kuri’un da Atiku ya samu, su ne Milyan 11,262,978. Don haka ba shi ne ya yi nasara ba, Buhari ne ya yi nasara da kuri’u milyan 15,191,847.

Martanin da INEC ta yi wa Atiku a kotu dai ya kai shafi 291, inda ta rika bi filla-filla ta na karyata ikirarin da ya yi

Share.

game da Author