INEC ta bayyana ranakun zaben gwamnan jihohin Bayelsa da Kogi

0

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta bayyana cewa za ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Bayelsa da Kogi, a ranar 2 Ga Nuwamba.

Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye ne ya bayyana haka, jiya Talata, a Abuja.

Ya ce bayan da Shugabannin INEC suka gudanar da taro, hukumar ta kuma fito da jadawalin yadda zabukan za su kasance, tun daga zaben fidda-gwani har zuwa zabe na game gari.

INEC ta ce za ta fitar da sanarwar fara hada-hadar zabe a ranar 1 Ga Agusta.

Sannan kuma duk jam’iyyar da ke da sha’awar shiga takarar zaben, to za ta yi zaben-fidda-gwani tsakanin ranar 2 Ga Agusta har zuwa 29 Ga Agusta.

INEC ta ce ta na bukatar kowace jam’iyyar da za ta shiga zaben ta aika mata da sunayen ejan-ejan din ta zuwa ranar 2 Ga Oktoba.

Jam’iyyu za su fara takara tun daga ranar 2 Ga Augusta har zuwa 31 Ga Oktoba.

BIN DIDDIGIN ZABEN 2019

INEC ta ce a cikin watan Mayu za ta yi gagarimin aikin nazari da kuma bin diddigin yadda zaben 2019 ya gudana.

Za ta bi diddigin yadda ita hukumar ta gudanar da zaben domin fahimta da gano wuraren da ta yi namijin korari, inda ta samu matsalolo da kuma cikas da kuma gano kalubalen da aka fuskanta a lokutan zaben.

Ta ce aikin zai shafu dukkan manyan ma’aikatan hukumar tare da fatan cewa abin da suka gano zai zama wani mataki wajen bi domin kafa Dokar Gyaran Zabe da ake son kafawa domin kara inganci da sahihancin zabe a nan gaba.

Share.

game da Author