Hukumar Tsaro ta Sojojin Saman Najeriya, ta bayyana kafa kwamitin binciken zargin da Sarakunan Gargajiya na Jihar Zamfara suka yi, cewa sojojin sama sun kashe fararen hula, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba.
Kwamitin wanda ke karkashin jagorancin Vice Marshal Idi Lubo, ya isa Jihar Zamfara tun a jiya Juma’a.
An yi zargin kashe jama’a ne a hare-haren da sojojin sama suka kai wasu wurare da nufin kakkabe ‘yan bindiga a wasu yankunan jihar.
Da ya ke zantawa da manema labarai a Gusau, a Hedikwatar Sojojin Quick Response Group, Lubo ya ce Hafsan Hafsoshin Sojan Sama, Air Marshall Sadique Abubakar ya damu kwarai bisa ga wannan zargi da aka yi wa sojojin sama, wadanda ke karkashin sa.
“Baya ga matukar nuna damuwar mu da mu ka yi, kasancewar mu wadanda aka dora wa nauyi da alhakin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya, to kuma ga shi mun zo nan domin mu binciki zargin da sarakunan gargajiya suka yi a Zamfara.
“Za mu bi mu gana da dukkan masu ruwa da tsaki a kan wannan al’amari, musamman gwamnatin jiha, jami’an tsaro, kai har ma da yankunan da aka yi zargin hare-haren sun shafa.”
Rahotanni sun tabbatar da cewa jim kadan bayan da takwagar kwamitin ta isa Gusau da yammacin Juma’a, ta gada da Daraktan Tsaro na Jami’an SSS, Sakataren Gwamnatin Tarayya a killace.
An tabbatar da cewa ta gana da su ne daya bayan daya.
Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka gabata ne majalisar Sarakunan Zamfara ta zargi Sojojin Operation Sharan Daji da kai hare-hare a cikin jama’a mazauna kauyuka, wadanda ba ‘yan bindiga ba.
Duk da cewa Hukumar Tsaron Sojojin Sama ta karyata, nan da nan sai sarakunan suka fitar da jerin sunayen wasu da ta ce an kashe,kuma ta lissafa wasu da ta ce an ji wa rauni.
Majalisar Sarakunan ta nuna cewa ba su kenan ba, sai dai a bar kaza cikin gashin ta kawai.
Wannan ya sa sojojin cikin damuwa, har aka kafa kwamitin bincike.