Hukumar kwastan ta kama tirela dankare da kwalaben Kodin 600

0

Hukumar kwastam dake kula da shiyar zone A a jihar Legas ta kama wata tirela dankare da kwalabe 600 na kodin.

Hukumar ta bayyana cewa kudin kwalaben kodin din za su kai Naira miliyan 240.

Jami’in hukumar Aliyu Mohammed ya sanar da haka yana mai cewa sun kama tirelan ne a Mile 2 hanyar Oshodo, jihar Legas.

” Direban tirelan ya tsere bayan ya hango jami’an kwastan sannan har yanzu babu wanda ke da masaniya kan inda tirelan za ta.

Muhammed yace tsakanin watan Fabrairu da Maris hukumar ta kama jakkuna 1000 na kwayoyin Tramadol da kudin sa ya kai Naira 250,00 a Sagamu jihar Ogun.

” Mun kuma kama buhuna 13,810 na shinkafar da aka hana shigowa da su kasar nan, kwayoyin maganin ciwon kirji da huhu da kudinsu zai kai Naira miliyan 105,600,000 da kuma sauran kayan da aka hana shigowa da su.

Bayan haka Muhammed ya kuma ce hukumar ta kama motar kamfanin Dangote dauke da buhunan shinkafa 800 da gwamnati ta hana shigowa da su kasan.

Share.

game da Author