Hukumar Hizba ta warware aure 312 cikin shekara 4 a jihar Jigawa

0

Shugaban hukumar Hizba ta jihar Jigawa Ibrahim Dahiru ya bayyana cewa hukumar ta warware aure akalla 312.

Hukumar ta ce ta warware auren yaran da aka yi musu aure ne alhalin basu kai ayi musu auren ba da wadanda aka yi musu auren dole a jihar.

Bayan haka kuma Dahiru ya ce an mayar da wasu yara almajirai ga iyayen su bayan an tabbatar da iyayen nasu nada karfin iya daukar dawainiyar su suka kyale su suna ta barace-barace.

” Mukan gayyaci iyayen da suka yi wa ‘ya’yan su auren dole mu tattau na da su sannan mu basu shawarwari da illolin dake tattare da yi wa ‘ya mace auren wuri da auren dole tun bata kai shekarun da zata iya jure zaman aure ba.

” Sannan kuma mukan sanar musu abin da doka ya ce game da yi wa mace auren dole da kuma aure bata kai lokacin ta yi ba.

Bayan haka Dahiru ya ce baya ga hada iyaye da ‘ya’yan su da suka tura karatun almajirci, mukan wayar musu da kai game da illar yin haka. Mu kan gaya musu cewa idan suka yi watsi da ‘ya’yan su da kin basu kula da ilimi za su girma su zama gagararru.

” Mukan yi musu bayanai karara game da illar tura ya’yansu Almajirci ba tare da an yi musu tanaji na yadda za su yi karatu cikin natsuwa, kula, tarbiyya da yalwa ba.

” Daga karshe sukan rika yawo ne kwararo-kwararo suna barace-barace. Ta dalilin haka kuwa sai kaga daga karshe yaro ya girma babu tarbiyya akasin abinda ya fita nema.

Share.

game da Author