Akalla mutane 19 ne suka motu a wani hatsarin mota da ya faru a Karamar Hukumar Gwaram da ke cikin Jihar Jigawa.
Hadarin ya faru a Gwaram Sabuwa, wajen 11:30 na ranar Talata.
Wanda aka yi hatsarin a gaban sa, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa daya daga cikin tayar motar ta gaba ce ta fashe, daga nan motar ta yi ta hantsilawa, har ta kama da wuta.
Ya shaida cewa dukkan wadanda suka mutu din sun konewar da ba a iya shaida su har a gane ko a tantance kowanen su.
“Na ga gawarwakin jarirai har shida, manne a jikin gawarwakin iyayen su.” Inji shi.
PREMIUM TIMES ta gano cewa motar wadda ke cin fasinjoji 19, an dankara mata fasinjoji har kusan 40, wadanda yawancin su mata ne da kananan yara.
Kakakin Yada Labarai na Rundunar ’Yan Sandan Jigawa, Abdul Jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, tare da yin karin bayanin cewa baya ga mutane 19 da suka mutu, wasu 21 kuma sun ji mumunan raunuka.
Ya ce motar ta taso ne daga garin Zango za ta Gadar Maiwa da ke cikin Karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi.
Dukkan fasinjojin an ce ‘yan uwa ne da abokan arziki, da ke kan hanyar su ta komawa gida bayan sun hakarci bikin aure.
Wadanda suka ji ciwo su na can kwance ana kula da su a asibitin Gwaram, cikin Jihar Jigawa.
Discussion about this post