A dalilin kara kaimi da gwamnatin Najeriya ta yi wajen ganin an kawo karshen ayyukan mahara da ‘yan ta’adda a garuruwan jihar Zamfara, sufeto janar din ‘yan sanda Mohammed Adamu ya bayyana cewa daga yau Lahadi gwamnati ta ba duk wani dan kasar waje dake hakon ma’adinai a jihar Zamfara ya tattara komatsan sa ya fice daga jihar.
Gwamnati ta ba duk wani dake da alaka da hakan awa 48 da su fice daga jihar ko kuma a kwace lasisin sa.
Bisa ga bayannan bincike da suka bayyana ga hukumomin tsaron kasarnan, an gano cewa atyukan hakan ma’adinai ne ainihin makasudin hayayyafa da tashe-tashen hankula da ake ta samu a jihar Zamfara din.
Baya ga irin wannan tashin hankula, ayyukan ta’addanci da yin garkuwa da mutane sun zama ruwan dare a jihar.
Sannan an gano cewa su kan su masu hakon ma’adinan sune suka ruruta fitana a jihar inda rikici a tsakanin su da ramuwar gayya ke sa a na ta yawan samun fitinu a jihar da rashin zaman lafiya.
A dalilin haka tuni har an kaddamar da sabuyar shiri na yaki da mahara da masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara da Jihar Kaduna.
A ranar Asabar ne, sojojin Saman Najeriya masu yin sintirin Operation Diran Mikiya, sun samu nasarar ratattaka mahara masu dimbin yawa a wani babban sansanin su da ke Ajiya, cikin Karamar Hukumar Birnin Magaji, Jihar Zamfara.
Daraktan Yada Labarai na Hukumar Sojojin Sama, Ibekunle Daramola ne ya bayyana a cikin wata takardar karin bayani da ya fitar ga manema labarai a Abuja.
Ya ce an kashe dozin da dama a dazukan cikin kauyukan Ajiya da Wonaka cikin Karamar Hukumar Birnin Magaji a Zamfara.