Gwamnati za ta bude fannin kula da kiwon lafiyar mata da yara kanana a kasar nan- Faisal Shuaib

0

Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) Faisal Shu’aib ya bayyana cewa gwamnati za ta bude fannin kula da kiwon lafiyar mata da yara kanana domin rage matsalar mace-macen yara da mata a kasar nan.

Faisal ya fadi haka ne ranan Litini a Abuja a wajen taron gabatar da matakan da gwamnati ta dauka domin rage mace-macen mata da yara kananan a kasar nan.

Ya ce bude fanni irin wannan na da mahimmancin gaske ganin cewa Najeriya na cikin kasashen duniyan dake yawan fama da mace macen mata da yara kanana.

Bincike ya nuna cewa mata 145 masu shekaru 15 zuwa 45 ne suke mutuwa a dalilin matsalolin haihuwa.

Sannan duk rana yara 2,300 ‘yan kasa da shekara biyar ne ke mutuwa a dalilin kamuwa da cututtukan da za a iya kawar da su.

Faisal yace lokaci ya yi da ya kamata a hada hannu gaba daya domin ceto rayukan mata da yara kanana a kasar nan.

Ya ce fannin za ta hada hannu da cibiyar kawar da cutar shan inna na kasa domin samun kudaden da za a bukata wajen ganin an samu nasara a akai.

Faisal ya kuma ce fannin za ta hada hannu da sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki, kungiyoyin bada tallafi da sauran mutane domin karkato da hankulansu wajen mahimmancin mara wa wannan buri baya.

A na su jawaban Sarkin Arugungu kuma shugaban kwamitin sarakunan gargajiya kan inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da shugaban hukumar kawar da cutar shan inna ta kasa Samaila Mera sun ce sarakunan gargajiya za su mara wa fannin baya domin samun nasarar inganta kiwon lafiyar mata da yara kanana a kasar nan.

” Za kuma mu horas da ungozoma domin inganta aiyukkansu sannan da wayar da kan maza magidanta wajen barin matayen su su rika zuwa asibiti domin yin awon ciki da haihuwa a asibiti.”

Share.

game da Author