GURUGUBJI DAMBEN DATTAWA: Sanata Lawan Da Ndume: Wa Za A Kai Kasa?

0

Sanata Ahmed Lawan da Ali Ndume dai ba sabbin-yanka-raken shiga Majalisar Dattawa ba ne. Sun jima ana gogawa da su.

A baya za a iya cewa ‘yan gida daya ne, wato Jihar Barno. Amma tun bayan kirkiro Jihar Yobe, sai Lawan ya raba hanya da Barno.

Ali Ndume ya kuma a Majalisar Tarayya ya na mamba. Har Shugaban Masu Rinjaye ya taba rikewa. Shi ma Ahmed Lawan haka. Kuma dukkan su su na APC ne.

A cikin garken manyan shanun Majalisar Dattawa, Lawal da Ndume duk manyan bijimin sa za a kira su. Kowa na jin kan sa, kowa na ji da karfin sa sannan kuma kowa na da girda-girdan gogaggun shanun da ke bayan sa.

Yayin da Lawan ke takama da manyan shanun cikin garken APC, wadanda suka ce lallai shi ne zai zame wa sauran shanu uwar-garken Majalisar Dattawa, shi kuma Ndume Goga ne mai shiga gaban jerin garken shanu, kuma Goga ne mai nike wa shanu turba.

Ndume ya na takama da manyan kosassun shanun da suka ci suka yi taiba, sannan kuma suka bijire wa duk wani Ardon da ya nemi ya yi huda da su ba tare da huda musu hanci ba.

Wadannan kosassun shanu sun tsaya kai da fata cewa ba za a yi amfani da su a noman daminar bana ba, matsawar a gonar Ahmed Lawan za a yi noman.

Su abin da su ke so kawai shi ne a kai su gonar Ndume, a can za su saki jiki, su yini kuma su kwana, ko da Ndume bai ba su ruwa da harawa ba.

Shugabancin Majalisar Dattawa dai ya zama abin da Hausawa ke cewa: Gurugubji damben dattawa, wai wanda ya fyace shi ya yi kuka.

To, ga shi dai gaggan shunu biyu, kuma dukkan su duna, sun fito kowa na son kujerar. Kuma kowa ya sai tayar da kura ya ke yi, ya na ruri.

Shin tsakanin Lawan da Ndume, wa zai ji tsoro ya hakura? Wa za a kayar idan aka bar su biyun kowa ya gwada karfi ya kwaci kujerar.

Wato kokawar da babu ruwan ka, dadin kallo gare ta.

Sanata Ahmed Lawan dai babu tababa yaron jagoran APC, Bola Tinubu ne. An sha fadar haka, kuma har yau bai taba fitowa ya nesanta kan sa da Bola Tinubu din ba, ballantana kuma ya karyata.

Bola Tinubu ne a sahun gaban ganin Lawan ya zama Shugaban Majalisar Tarayya, dama kuma shi ne ya jajirce a 2015 ya ce Lawal din ne za a zaba.

Na biyu kuma shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa baki daya, Adams Oshimhole, wanda shi ne ke shiga-nan-fita-can domin ganin lallai hakar sa ta cimma ruwa, Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

Rukunin mutane na uku da ke goyon bayan Lawan, su ne sanatocin APC, wadanda ba su iya sauyawa daga abin da jam’iyya ta ce a yi, kuma su na goyon bayan Lawan.

GAGGAN DA SANATA LAWAN KE TAKAMA DA SU

Sanata Ahmed Lawan dai babu tababa yaron jagoran APC, Bola Tinubu ne. An sha fadar haka, kuma har yau bai taba fitowa ya nesanta kan sa da Bola Tinubu din ba, ballantana kuma ya karyata.

Bola Tinubu ne a sahun gaban ganin Lawan ya zama Shugaban Majalisar Tarayya, dama kuma shi ne ya jajirce a 2015 ya ce Lawal din ne za a zaba.

Na biyu kuma shi ne Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa baki daya, Adams Oshimhole, wanda shi ne ke shiga-nan-fita-can domin ganin lallai hakar sa ta cimma ruwa, Lawan ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

Rukunin mutane na uku da ke goyon bayan Lawan, su ne sanatocin APC, wadanda ba su iya sauyawa daga abin da jam’iyya ta ce a yi, kuma su na goyon bayan Lawan.

GAGGAN DA KE GOYON BAYAN NDUME

Ko shakka babu Sanata Ali Ndume na da magoya baya da yawa, masu son ganin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.

Rukunin farko, akwai ‘yan APC masu ganin bai yiwuwa a ce tsofai-tsofai da su, a hana su yin zaben shugaban majalisa, kamar yadda doka ta tanada.

Su na jin haushin don me haka kawai Adams Oshimhole zai maida su wasu kananan yara, kamar daliban sakandare, ga shi kuma shi bai ma taba yin sanata ba?

Akwai kuma gaba dayan sanatocin PDP, wadanda tabbas ba su goyon bayan Sanata Ahmed Lawan. Za su so a ce wani wanda ya yi wa APC tawaye ne ya zama shugaban majalisa.

Ko da yake su ma na PDP din, akwai rade-radin cewa idan ta yi rincimi, za su tsaida dan takarar da wasu hasalallun sanatocin APC za su hadu da na PDP, a zabe shi.

A nan ana nufin akwai yiwuwar idan rikicin shugabancin ya kara tirnikewa, zai iya komawa a hannun PDP, kamar dai yadda aka yi a 2015.

JERIN WADANDA SUKA TABA RIKE MAJALISAR DATTAWA

Nnamdi Azikwe (NCNC): 1960

Dennis Osadebe (NCNC): 1960 – 1963

Nwazu Orizu (NCNC): 1963 – 1966

Joseph Wayas (NPN): 1979 – 1983

Iyorchia Ayu (SDP); 1992 – 1993

Ameh Ebute (SDP): 1993

Evan Enweram (PDP): 1999

Chuba Okadigbo (PDP): 1999 – 2000

Anyim Pius Anyim (PDP): 2000 – 2003

Adolphos Wabara (PDP): 2003 -2005

Ken Inamani (PDP): 2005 – 2007

David Mark (PDP): 2007 – 2015

Bukola Saraki (PDP): 2015 Zuwa Yau

Share.

game da Author