‘Gunkin Ife’ na Yarabawa ne salsalar kirkiro Google -Inji Ooni na Ife

0

Babban Basaraken Kasar Yarabawa, Ooni na Ife, ya ce gunkin ‘Ife’, ko dodon ‘Ife’, shi ne musabbabin sabuwar hanyar fasahar neman bayanai ta zamani, wato Google.

Basaraken ya furta haka ne lokacin da ya ke zagayawa da manema labarai ganin ci gaban da aka samu wajen shirye-shiryen gudanar da gagarimin Taron Cibiyoyin Bude Ido Kan Sabbin Kirkire-kirkire da za a gudanar a Ile -Ife, a ranar 24 Ga Afrilu.

Ooni na Ife, ya hakkake cewa ba don akwai tsarin surkullen neman sa’a daga wajen Ifa ba, tun dubban shekaru da suka shude, to da BA za a iya kirkiro Google ba.

Ya ce mutanen dauri kan yi surkullen ‘Odu Ifa’, domin su nemi sa’a a duk ayyuka ko wani lamari da suka sa a gaba.

Sai ya ce to shi ma Google a yanzu aikin da kenan, idan ka na neman wani bayanin da ya wuce, ko wanda zai zo nan gaba, to Google ake shiga a samu Karin bayanin.

Ya ce ‘Odu Ifa’ surkulle ne da ake yi wa dodo ko gunkin Ife domin ya samo maka sa’a ga Ubangiji. Kuma kasashen Afrika ta Yamma sun dade su na wannan surkullen neman sa’a ga ‘Ifa’.

“Sun maida shi wata hanyar samun sako ko bayanai daga ubangijin su a tsarin na gargajiya, kamar yadda a yanzu Google ya zama hanyar bincike da neman karin bayani na zamani.

A karshe ya yi kira da a kara yin riko sosai da igiyar addinin gargajiya, wanda ya ce bautar addinin gargajiya za ka iya hada ta da bauta irin ta manyan addinai da ake yi a yanzu.

Share.

game da Author