Tashin wata gobara a jiya Asabar ta kone matsugunan ‘yan gudun hijira ha biyu a Barno, Arewa maso Gabacin Najeriya.
Wutar ta tashi a sansanin Flatari da na Nguro duk a cikin Karamar Hukumar Monguno a Jihar Barno.
Kakakin Yada Labarai na Hukumar Kai Daukin Gaggawa na Arewa maso Gabas, Abdulkadir Ibrahim ne ya bayyana haka yau Lahadi.
Ya ce gobarar ta shafi gidaje 20, ta kone matsuganai da bukkokin masu gudun jira 120, tare da lalata wasu gidaje 77 a sansanin Nguro.
Ya kara cewa mutane 371 ne suka yi sararar muhallin su.
A karshe ya ce NEMA za ta gaggauta tantance wadanda gobarar ta shafa, domin a kai musu agaji.