Gobara ta cinye shaguna 27 a kasuwar Kurmi, Kano

0

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saidu Mohammed ya bayyana wa kamfanin dillancin Labarai cewa akalla shaguna 27 ne wuta ta cinye a kasuwar Kurmi yan-nama dake jihar Kano.

Saidu ya ce wani Ado Musa ne ya kira hukumar ta waya da misalin karfe 4:30 na asuba ya gawa musu cewa kasuwar ta kama da wuta.

” Muna jin haka sai muka gaggauta aikawa da jami’an mu wannan kasuwa domin kashe wannan wuta. akalla shaguna 27 ne suka kone kurmus, sannan wasu guda 8 basu kai ga konewa gabadaya ba.

A karshe Saidu ya yi kira ga ‘yan kasuwa da su tanaji kayan kashe gobara na gaggawa a shagunan su, kamar su bargunana, bokatan kashe wuta da sauransu.

Share.

game da Author