Wata Kungiyar Dattawan Yankin Arewa ta Tsakiya, mai suna ‘North Central Elders Forum’ (NCEF), ta bijire wa jam’iyyar APC bisa umarnin da ta bayar cewa Hon. Femi Gbajabiamila ne zai zama Shugaban Majalisar Tarayya.
Cikin wata takardar da suka raba a taron manema labarai jiya Litinin a Abuja, NCEF ta ce ba su yarda a tirsasa Gbajabiamila a matsayin Shugaban Majalisar Tarayya ba.
Dattawan sun ce su na goyon bayan Hon. Idris Wase a matsayin shugaban majalisa.
Sun kafa dalilan cewa an dade ana tauye Yankin Arewa ta Tsakiya a rabon manyan makamai a Majalisar Tarayya.
Dalili kenan suka ce sun goyi bayan Idris Wase ya zama shugaba, kasancewar sa kuma ya fi sauran yawan shekaru, sannan kuma shi ne Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye a Majalisa.
Mai Magana da Yawun Dattawan NCEF, Muhammad Ari-Gwaska, ya ce ya na da tabbacin daya dan Yankin su mai takarar, wato Hon. Umaru Bago, zai janye wa yayan sa Idris Wase.
Daga nan sai Gwaska ya roki dukkan shugabannin APC da su dubi Allah, su yi adalci, su nuna dattako, kyatatawa, gaskiya, nuna hadin kai da kuma irin yadda Arewa ta Tsakiya ke taka rawa wajen kafa gwamnati, bar mata wannan mukami a wannan zangon dimokradiyya.
Ya zuwa lokacin da aka gudanar da taron dai Idris Wase bai kai ga cewa zai fito takara ba.
Sauran masu takarar mukamin shugabancin Majalisar Tarayya sun hada da: Femi Gbajabiamila, Muktar Betara, Abdulrazak Namdas da Umar Bago.