GARKUWA DA MUTANE: Majalisar Dattawa ta gayyaci Sufeto Janar yin bayani

0

Majalisar Dattawa ta bayyana damuwa da rashin dadin yadda ake yawan garkuwa da mutane a fadin kasar nan, wanda hakan ya fusatar da su har suka gayyaci Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu da gabatar da kan sa domin yinn karin bayani.

Majalisa ta ce an gayyace shi ne domin ya yi bayanin tare da tattauna hanyoyin da za a magance matsalar baki daya.

Wannan gayyata da aka yi masa ta na daya daga cikin matsalolin da aka tattauna za a bi domin ganin an magance abin da su ka kira “kisan ba gaira ba dalili da ake yi tare da garkuwa da jama’a a fadin kasar nan.”

Musamman sun kuma yi magana a kan sace wata Bsturiya ’yar kasar Birtaniya da aka yi makon da wuce a wani wurin shakatawa a jihar Kaduna.

Sanata Shehu Sani ne ya bayar da kudirin bukatar a gayyaci Sufeto Janar Adamu.

An sace wata ‘Yar Birtaniya mai suna Faye Mooney wadda ma’aikaciyar agaji ce a ‘Kajuru Castle’, wani wurin shakatawa.

Mahara sun kashe Mooney da wani mai suna Matthew Oguche dake kungiyar agaji a INSO, sannan kuma suka yi garkuwa da wasu mutane uku.

Sanata Sani ya ce idan ba a tashi tsaye ba, to abin zai gagari kowa, domin duk da yawan kashe mutane, garkuwa da kone gidaje da kauyuka da ake yi, har yau ba a daure kowa daga cikin wadanda ake kamawa da aikta laifin ba.

“Daga nan ya kara da cewa maimakon a ce ana samunngalaba a kan su, sai ma ‘yan bindigar ne a kullum ke ta kara cika-baki cewa sun ne ke yin galaba saboda sun fi jami’an tsaro manyan makamai.”

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, ya ce ba wannan ne karo na farko da aka taba kashe dan kasar waje a harin garkuwa da mutane ba.

Shi ma ya nuna matukar damuwar sa tare da neman ganin an magance matsalar kafin ka gagara magancewa.

Share.

game da Author