Mutanen yankin Arewa Maso yammacin Najeriya ba su taba fadawa cikin halin kakanikayi, rudani, tashin hankali da dimaucewa kamar a yanzu ba a dalilin ayyukan mahara da masu yin garkuwa da mutane.
Fashi da makami, yin garkuwa da mutane sun zamo ruwan dare a wannan yanki. Mutanen Jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina har da Sokoto suna matukar dandana kudar su domin kuwa tafiya zuwa wasu biranen yana neman ya gagari jama’an Najeriya.
Babban Titin da ya hada yankin Arewa kakaf da babban birnin tarayya, Abuja da kuma yankin kudancin Najeriya ta zama ‘Horo’ ga matafiya.
Duka wani da ke aiki a Abuja, ko kuma dan kasuwa ya kan fada cikin zullumi da tashin hankali idan har ya kama zai bi wannan hanya ta Abuja zuwa Kaduna.
An mai da mutane kamar awaki, mahara sukan fito bakin titi, ido na ganin ido, wato da rana tsaka su tattare motoci su kashe na kashewa sannan su tafi da wasu iya son ransu. Sukan dauki sama da mintuna 30 suna sheke ayar su ba zaka ga wani jami’in tsaro ba, sannan ba za ka ji wai yau an far musu a lokacin da aka sace mutanen an kwato su daga masu garkuwan ba.
Haka dai akwana a tashi, maganan garkuwa da mutane ya zama sana’a domin idan ba haka ba ace an yi yau, anyi gobe an yi jibi duk kuma lafiya lau sai dai kawai aje a nemo kudin diyya a biya ba tare da an bi sahun su an kamo su ba sannan a hukunta su kowa yagani.
Sannan wadanda ake kamawa ma idan har aka tafi dasu ba za aka ji abinda aka yi musu ba.
Sarakunan Arewa da Kungiyar Dattawan Arewa
Lokaci na neman ya kuri wa shugabannin yankin Arewa domin idan har abin yafi karfin tattare mutane a tituna, zai daka tsalle ne ya fado har gidajen su da ya’yan su.
A yau an kai ga ba zaka iya yin mua’amula da duk wani naka dake zama a garin Birnin Gwari ba, jihar Kaduna domin kuwa wannan hanya ta Birnin Gwari ta yi kaurin suna a yankin Arewa. Yin garkuwa da mutane yayi matukar zama sana’a a wuraren wannan yanki.
Jihar Zamfara da jihar Katsina sun bi sahun Birnin Gwari. A kullum sai kaji an biyo mutane har gida ana tafiya da su cikin kungurmin daji wai an yi garkuwa da su.
Ya kamata a yi taron gaggawa ta musamman domin wannan matsala da ake fama da shi. Dole sai sarakuna iyayen al’umma, Malaman addinai da masu fada a ji sun fito sun yi kira ga shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya karkato ya maido hankalinsa wajen ganin an yi wani abu akan haka cikin gaggawa idan ba haka ba kuwa shikenan sai kuma yadda Allah yayi da mutane.
Muna kira ga Baba Buhari da ya dubi mutanen wannan yanki na Arewa da idon rahama, ya tausaya wa mutanen Arewa, A matsayin sa na shugaban mu duka ya mike tsaye don ganin an fatattaki wadannan miyagun mutane a hanyoyin kasar nan musamman babban titin Abuja-Kaduna da shine mahadar Arewa da kudancin Najeriya da ake amfani da shi.
Discussion about this post