Wani likitan yara a asibitin koyarwa na jami’ar Benin (UBTH) Okusola Olusola ya yi kira ga iyaye da su gujewa ba ‘ya’yan su maganin zazzabin cizon sauro ba tare da an yi gwaji ba an tabbatar da hakan.
Olusola ya yi wannan kira ne ranar Litini da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a jihar Legas.
Ya ce uwaye kan yi wannan kuskure ne wajen gaggawan ganin ‘ya’yan su sun warke ba tare da an yi gwaji ba an tabbatar.
” Ba yara maganin zazzabin cizon sauro ba tare da an tabbatar suna dauke da cutar ba na iya hana maganin yin aiki a jikin su koda sun kamu da cutar nan gaba sannan wai don aba yaro saboda rigakafi duk ba zai yi tasiri ba.
Olusola yace ba laifi bane idan uwa ta yi tanadin maganin a gida amma kuma kuskure ne a dirka masa maganin ba tare da an yi gwaji ba.
” Akwai yiwuwar cewa zafin jikin da kan sami yara mura ne ko kuma zazzabin fitar da hakora ne kawai amma ba zazzabin cizon sauro ba.