Fyade:’Yan sanda sun kama uba da da da aka kama da laifin dirka wa ‘yar shekara 14 ciki

0

A ranar Litini ne kotun majistare dake jihar Legas da gurfanar da wani magidanci Kabiru Oke mai shekaru 44 da dansa Oke Faruq mai shekaru 19 da laifukan yin fyade da dirkawa wata ‘yar shekara 14 ciki.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bala Elkana ya shigar da kara a gaban kotu inda ya bayyana wa kotu cewa Kabiru ya fara lalata da wannan yarinya ce a watan Oktoba 2018 shi kuma dan sa Faruq a watan Janairu 2019.

” Mahaifiyar yarinyar ce ta kawo karar fyaden da Faruq da Kabiru suka yi wa yar ta ofishin mu bayan ta gano cewa yarinyar na dauke da ciki.

” Binciken da muka gudanar ya nuna cewa Kabiru mijin kanwar mahaifiyar yarinyar ne sannan mahaifiyar yarinyar ta kai ‘yarta gidan Kabiru dake Egbeda domin kanwar ta ta sami ‘yar zaman daki.

Elkana ya ce za a ci gaba da shari’ar ranar 13 ga watan Mayu sannan Kabiru da Faruq za su zauna a kurkukun Kirikiri har sai an kammala shari’ar a kotu.

Bayan haka rundunar ‘yan sandan ta kuma kama wani Marainerume Alfred mai shekaru 45 da laifin yi wa ‘yar shekara 14 fyade shima.

Elkana yace mahaifiyar yarinyar ce ta kawo kara ofishin ‘yan sandan bayan yarinyar ta sanar da Kakan ta halin da take ciki.

” Bincike ya nuna cewa Alfred ya fara yin lalata da wannan yarinya ce tun a watan Mayu 2018 har zuwa Maris din 2019.

” Alfred yana da shagon da yake siyar da fina-finan Nollywood sannan ya kan rudi wannan yariya ta shiga shagonsa a lokacin da take hanyar dawowa daga makaranta. Bayan ya gama lalata da ita sai ya bata ruwan gishiri da wasu kwayoyi ta sha domin kada ta dauki ciki.

Elkana yace har yanzu dai rundunar na gudanar da bincike sannan da zaran sun kammala zasu gabatar da Alfred a kotu.

Share.

game da Author