A yammacin Lahadi ne magoya bayan kungiyar Manchester United suka yi tsaye sototo su na kallon yadda kungiyar Everton ta kwarara mata kwallaye har guda 4.
Ko ta ina za a kalli wasan, za a iya cewa Everton ta yi bajintar da ta disashe duk wani kaifin ‘yan wasan Manchester, wadanda aka rika yin wasan kura da su a cikin fili.
Magoya bayan Everton za su kwana da farin ciki, ganin cewa sun kara rike waManchester kafa, yadda idan ta yi sake, to ba za iya fitowa gasar Champions League na 2019/2020 ba.
REAL MADRID ta lallasa kungiyar Atletico Bilbao da ci uku. Duk Karim Benzama ne ya ci kwallayen uku. Ya kafa tarihin cewa bait aba cin kwallaye 21 ba a kaka daya a Madrid, sai a yau.
Sannan kuma ya fi kowane dan wasan Turai yawan cin kwallaye da kai cikin kakar wasa daya. Kwallaye 11 ya ci da kai a wannan kakar ta La Liga.
CRISTIANO RONALDO shi ma a jiya ya kafa tarihin cewa shi ne dan wasa na farko da ya taba cin kofin Premier League, na La Liga da kuma na Seria A. Ronaldo na da alamun zai tsaya ya kara wata kakar gasar a Juventus, wadda ta dauki kofin Seria A a jya Asabar.
LIVERPOOL FC ta bi Crystal Palce har gida ta jefa maya kwallaye biyu, wadanda suka maida ta na daya a Premier League. Sai dai kuma Manchester City ta rike mata kafa.
A yauzu dai a tsakanin su duk wanda ya bari aka yi nasara a kan sa, to tabbas babu shi babu cin kofin Premier League.