Gwamman jihar Kaduna ya umarci duka wadanda ya nada a lokacin da ya zama gwamna a 2015 da su tattara nasu-ina-su nan da 30 ga watan Afrilu.
El-Rufai ya bayyana haka ne a takarda da kakakin sa Samuel Aruwan ya saka wa hannu a garin Kaduna.
El-Rufai ya ce wannan sanarwa ya shafi duka kwamishinoni da masu bada shawara ta musamman da ya nada a jihar.
Suma shugabannin ma’aikatun gwamnati na jihar duk sun fada cikin wannan tankade da rairaya.
Sai dai kuma sanarwan ta ce wannan umarni bai hada da wadanda aka yi wa sabbin nadi ba a makonni da suka wuce da suka hada da Kwamishinan Kudi, wato tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Muhammmad Saidu da sauran su.