Shafin Dubawa (dubawa.org) da ta shahara wajen yin binciken kwa-kwaf ta bunciko gaskiyar wani bidiyo da ya karade shafunan sada zumunta ta Facebook da wasu kafafe cewa wai El-Rufai ya ce Buhari ya san wadanda ke ruruta wutan rashin zaman lafiya da ake fama dashi a jihar Zamfara.
Binciken da Dubawa (dubawa.org) tayi sannan ta wallafa a shafinta ya tabbatar da haka sai dai ta ce a hakikanin gaskiya El-Rufai ne a wannan bidiyo kuma yayi wadannan maganganu amma ba ga gwamnatin Buhari yayi ba.
” El-Rufai ya bayyana cewa yana kalubalantar gwamnati da ta fito ta bayyana hukumomin tsaro su fito su bayyana sunayen wadanda suke da hannu a wannan tashin-tashina da ake fama da su. Kuma in gaya muku ku sani, shugaban kasa ya san wadanda suke aikata wannan tashin hankali.” Kamar yadda ya bayyana a bidiyon.
Binciken kwa-kwaf da Dubawa (dubawa.org) ta yi ya nuna karara cewa wannan bidiyo an dauke shi ne tun a 2013 a lokacin da yake hira da gidan talabijin din TVC.
Hakan ya nuna cewa ba yanzu bane El-Rufai ya yi wadannan maganganu. Yayi su shekaru shida da suka wuce ne tun kafin ya zama gwamnan jigar Kaduna.
GASKIYAR MAGANA: El-Rufai baice Buhari ya san wadanda ke kitsawa da kuma hannu a rashin zaman lafiyan da ya yi wa jihar Zamfara rawani a ka.