Kungiyar Tarayyar Turai ta ce a halin yanzu daga kasashen duniya ana yi wa Najeriya kallon wata kasa wadda ake rububin samu da fataucin karuwai, safarar wadanda ake tilastawa yin ayyukan wahala da kuma samun sassan jikin mutum.
Sannan kuma Tarayyar Turai (EU), ta ce za ta goya wa Najeriya baya wajen ganin ta magance wadannan mugayen illoli a cikin al’umma.
Shugaban Tawagar EU a Najeriya da kuma Kasashen Afrika ta Yamma, Ketil Karlsen ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwac da jami’in yada labarai na kungiyar mai suna Modestus Chukwulaka ya fitar jiya Asabar.
Karlsen ya yi wannan bayani ne a jiya Labara a Lagos, jim kadan bayan jirgi na 64 ya dawo da ‘yan Najeriya wadanda ke zaune a wasu kasahe na Turai daban-daban.
Daga nan kuma ya ce Tarayyar Turai na aiki kafada-da-kafada al’ummar yankuna domin ganin an samar da wani yanayin tattalin arzikin da zai kawar da yawan hijirar da ake yi da yawan fasa-kwauri sannan kuma a samar da yanayi na ayyukan dogaro da wadanda ke dawowa cikin Najeriya daga Turai za su iya samun ci gaba da rayuwar su.
EU kuma za ta bada hadin kai domin ganwa da kawo karshen ainihin babban dalilin da ke sa ake yawan samun yin hijira daga Najeriya zuwa kasahen Turai da sauran wuraren.
Karlsen ya ce ba wai EU so ta ke ta hana jama’a yin kaura ko hijira ba kwata-kwata.
Cewa ya yi EU ta na son idan ma har mutum zai yi hijira, to ya kasance don rajin kan sa da bukatar kan sa ce zai yi, amma ba wai saboda kuncin rayuwa ko neman kudi ido rufe ko ma ta wace hanya a kasashen Turai ba.
Ya ce an samu nasarar dawo da ’yan Najeriya har 12,974, wadanda 1,158 an maido su ne a cikin 2019.
A karshe ya ce Tarayyar Turi ce da kan ta ke daukar nauyin jigilar maido da ’yan Najeriya gida, kare rayukan su da kuma ganin sun dawo don kan su. Sannan kuma ta sake karfafa musu karfin sake samun madogara a nan gida Najeriya.
Discussion about this post