A yau Alhamis ne Babbar Kotun FCT da ke Maitama, Abuja, ta tsaida ranar 24 Ga Mayu, 2 cewa za ta saurari karar neman biyan diyya da tsohon Kakakin Yada Labarai na Boko Haram, Ali Konduga ya kai Hukumar Tsaro ta SSS.
Ali Konduga, wanda tsohon sakataren yada labarai ne na Boko Haram kafin a kama shi, ya shigar da kara ya na neman diyyar naira 500,000 daga SSS, saboda sun tsare tsawon karin wasu shekaru uku bayan cikar wa’adin da aka yanke masa hukunci.
Lauyan Konduga mai suna Mohammed Tola ne ya shigar da kara a madadin Konduga, inda ya maka Babban Daraktan SSS da kuma Antoni Janar, wato Ministan Shari’a kotu,
Tola ya ce wa kotu an tauye wa Konduga wanda ya ke karewa hakkin sa a matsayin sa na dan Adam kafin a sake shi cikin 2016.
Wata Kotun Majistare ce a Abuja ta yanke wa Konduga hukuncin daurin shekaru uku a cikin 2011. An same shi da laifin razana mutane.
A karar da a lauyan Konduga ya shigar, ya ce an tsare shi a gadirun din SSS maimakon a kai shi gidan kurkuku ya yi zaman wa’adin sa a can.
Ali Konduga ya ce an tsare shi saboda gwamnati kawai ta na so a yi amfani da shi wajen bayar da shaidar tabbar da zargin ta’addanci a kan Sanata Ali Ndume, a Babbar Kotun Tarayya a lokacin.
Daga nan ya ci gaba da cewa, ya zuwa lokacin da aka sake shi, ba a taba kiran sa domin bayar da shaida a batun Ndume ko ma a kan wani ba.
Konduga ya ce an dauke shi an kai shi ofishin SSS na Maiduguri a ranar 8 Ga Satumba, 2016, daga nan aka sake shi a washegari, 9 Ga Satumba, 2016.
Ali Konduga ya ce SSS sun bai wa iyalan sa naira 700,000 a lokacin da aka sake shi, suka shaida musu an bayar da kudin ne domin a nemar wa Ali maganin rashin lafiyar da ke damun sa.
Ali Konduga ya ce wannan ihisanin kudi da aka bai wa iyalan sa sun nuna cewa SSS na sane da cewa ya cancanci a biya shi diyya kenan.
Ya kuma ce daga nan SSS ba su kara biyan sa ko sisi ba, tun bayan naira 700.000 din.
Har ila yau, Kwanduga ya ce bayan an sake shi a cikin 2016, wasu gungun mutane sun tare shi sun lakada masa duka, har suka ji masa ciwo a kan sa.
Ya ce sanadiyyar ciwon da aka ji masa ne Jami’an Ofishin ’Yan Sanda na GRA da ke Maiduguri suka dauke shi, suka rike shi sun a kare lafiyar sa.
Daga nan inji Konduga, an maida shi Asibitin Tababbu da ke Maiduguri.
Konduga ya nemi Hukumar SSS ta ba shi hakuri a cikin jaridun kasar nan guda uku.
Daga nan kuma ya roki kotu da ta tilasta wa SSS da Ministan Shari’a cewa kowanen su su biya shi naira 500,000 kudin diyyar tsare shi da aka yi ba bisa hakkin da shari’a ta ce ba.