Kakakin Majalisar Tarayya, Yakubu Dogara, ya bayyana cewa matsawar aka tirsasa wa Majalisar Dattawa da ta Tarayya shugabannin da zabin da rayukan su ke so ba, to shugabancin ba zai yi karko ba.
Dogara ya ce Majalisar Tarayya zababbun mutane ne kuma gogaggu a fannonin rayuwa daban-daban, don haka a bar su su zabi wanda ya dace, kuma a yi zaben a bisa tsarin da ya dace.
Ya yi wannan furuci ne a jiya Litinin, lokacin da ya ke jawabi wurin bude taron sanin-makamar-aiki ga zababbun Majalisar Dattawa da na Tarayya, a Abuja.
Dogara ya ce ya kamata zababbun ‘yan majalisa da za su shiga wannan majalisa ta zango na 9, su tsaya su dubi dukkan ‘yan takarar shugabanci, sannan su zabi cancanta, nagarta da kuma kwarewa da gogewa.
Ya kuma ja hankulan mambobin da su dauki darasi daga abubuwan da suka rika faruwa a majalisa a baya, a duk lokacin da aka kakaba shugabanni ta kan katanga.
Ya sake tunatar da su cewa za su shafe shekaru hudu a majalisa su na fama da gudanar da ayyukan jama’ar da suka zabe su daga sassa daban-daban na kasar nan.
“Mu za mu iya cewa mun dade a majalisa, mun ga jiya kuma mun ga shekaranjiya jiya a majalisa. Saboda haka idan aka kakaba wa mambobin mu shugabannin da ba su yi musu ba, shirin ba zai dore ba zai watse.”
Dogara ya zama Kakakin Majalisa a karkashin jam’iyyar APC cikin 2015, bayan da ya kayar da Femi Gbajabiamila a takara.
A yanzu dai uwar jam’iyyar APC mai rinjayen mambobi, ta tsaida Gbajabiamila a matsayin wanda ta ke so ya zama Kakakin Majalisa.
Sai dai kuma akwai wadanda suka yi wa wannan umarni na shugabannin APC tutsu, suka ce sai an yi zabe.