DAURE IG WALA: Yadda dan rajin kare hakkin jama’a ya kasa kare kan sa a kotu

0

Mai Shari’a Yusuf Halilu na Babbar Kotun Tarayya reshen Abuja, ya yanke wa I.G Wala daurin shekaru bakwai a gidan yari, saboda kama shi za laifin yi wa Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa kazafin wawurar bilyoyin kudade.

Jiya Litinin ne mai shari’ar ya daure Ibrahim Wala bayan an same shi laifin kasa bayar da gamsasshiyar hujjar kazafin wawurar kudi har naira bilyan 3 da ya yi wa Shugaban Hukumar Alhazai, Abdullahi Mukhtar. An kuma same shi da laifin kafa kungiya, tare da jagorancin kungiyar mai suna CATBAN, inda ya jagoranci zanga-zanga kan shugaban hukumar Alhazai, alhali kungiyar ba ta da rajista.

Sufeto Janar na ’Yan Sanda ne ya shigar da karar I G Wala a gaban kotu, kuma an zarge shi da bata wa shugaban hukumar suna, ta hanyar yi masa kazafin abin da bai aikata ba.

Laifuka ukun da aka kama shi da laifi sun hada da tara gangamin jama’a ba tare da bin ka’idar doka ba, tunzira jama’a da kuma bata suna.

Tun da farko dai an gurfanar da Wala ne bayan da Abdullahi Mukhtar, Shugaban Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ya kai koken sa a gaban ‘yan sanda.

Mukhtar ya ce Wala ya rika amfani da shafin sa na Facebook ya na tunzira jama’a a kan sa, tare da bata masa suna da zubar masa da kima da ta hukumar da ke shugabanci gaba daya.

Mai Shari’a Halilu ya ce kungiyar Wala mai suna ‘Citizens Action To Take Nigeria Back (CATBAN)’, ba ta da rajista, don haka haram ne ta gudanar da wani taro.

An yanke masa hukuncin shekara bakwai a kan wannan laifin.

Sai kuma an same shi da laifin tunzira jama’a, wanda ya kauce wa sashe na 114 na dokar panel code.

A nan ma an yanke masa hukuncin shekaru uku a kurkuku.

Mai Shari’a ya kuma gamsu da cewa Wala ya bata wa Mukhtar suna, tunda ya zarge shi da laifin azurta kan sa da naira bilyan 3 daga aikin Hajji na 2017, abin da shi Wala ya kasa gabatar da shaida.

“Ina takardun shaidar da ka ce ka na da su masu nuna Shugaban Hukumar Alhazai ya ci naira biliyan 3?

“Me ya sa wanda ake argin ya kasa bayar da shaidar da ya ce ya na da ita tunda har an kawo shi kotu, kuma an zo wurin yanke hukunci?” Inji Mai Shari’a Halilu.

Halilu ya ce tunda Wala ya kasa gabatar da shaida, hakan ya rage wa kotu wahalhalu da jan lokacin tirka-tirkar shari’a tsawon lokaci.

A nan kuma sau ya yanke masa hukuncin shekaru biyu a kurkuku.

Sai dai kuma da yake dukkan hukuncin uku za su tafi ne bai daya, hakan na nufin Wala ba shekaru 12 zai yi a kurkuku ba.

Zai shafe shekaru bakwai ne kawai. Sai fa idan ya yi nasara idan ya daukaka kara.

Za a ci gaba da tsare shi a gidan kurkukun Suleja.

Wala fitaccen dan rajin kare dimokradiyya da hakkin jama’a ne da ya yi suna wajen nuna rashin goyon bayan abin da ya ke gani ba daidai ba a fadin kasar nan.

Sannan kuma ya na a sahun gaban masu rajin tallata Buhariyya a Najeriya.

Share.

game da Author