Wasu dandazon mabiya Shi’a, almajiran Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, da a Turance ake kiran su IMN, sun karya kofar shiga Majalisar Tarayya ta farko, a yau Laraba, suka shiga cikin harabar.
Da farko dai sun je bakin kofar ne da ranar yau Laraba, suka yi kokarin karya kofar, amma jami’an tsaro suka shaida musu cewa baa i yiwu su samu yin magana da ko da daya daga cikin Mambobin Majalisar Tarayya din ba.
Ana cikin haka ne wannan furuci ya fusata su, su ka yi kumumuwa da kukan-kura, suka karya kofa da tsiya, suka kutsa cikin majalisar.
Wannan lamarin shiga majalisa da karfin tsiya da mabiya Shi’a suka yi, ya tilasta Mataimakin Shugaban Majalisar Tarayya, Yusuf Lasun yin sanarwar rufe zaman majalisar da gaggawa, tare da yin sanarwar cewa mabiya Shi’a ne suka antayo cikin majalisar.