Dalilin da ya sa Buhari ba zai sauke ministocin sa ba – Lai Mohammed

0

Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya bayyana cewa babu wani shiri da Shugaba Muhammadu Buhari ke yi a yanzu na sallamar ministocin sa daga aiki.

Cikin makon jiya ne Shugaba Buhari ya umarci dukkan ministocin sa su aika da cikakken bayanin ayyukan da suka gudanar na tsawon wa’adin mulkin su.

Ya umarce su da su aika da su zuwa ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Wannan sanarwa da aka yi, ta sa an rika hasashen cewa watakila Buhari ya shirya sauke ministocin na sa nan ba da dadewa ba, kafin ranar 29 Ga Mayu, ranar sake rantsar da Buhari.

Sai dai kuma a yau Alhamis, Lai Mohammed ya shaida wa manema labarai na Fadar Shugaban Kasa cewa “Ministoci na nan daram, babu wani shirin tsige su ko sauke su da ake yi. Domin nan da ranar 22 Ga Mayu ba za mu yi taron yi wa juna bankwana da murnar kammala zangon 2015 zuwa 2019 lafiya.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya shugabanci taron Majalisar Ministoci da aka gudanar yau Alhamis a Fadar Shugaban Kasa.

Share.

game da Author