Wani dalibi mai suna Kolapo Olowoporoku da ke Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife, ya kashe kan sa saboda ya gaji da rubuta jarabawa ya na faduwa.
Dalibin wanda ke maimaita jarabawa daya ta karshe har tsawon shekaru biyu kenan a fannin Kimiyyar Kwamfuta, ya kamata a ce ya fita shekaru biyu da suka gabata, amma wasu darussa biyu suka zame masa karfen-kafa.
PREMIUM TIMES ta gano cewa abokan karatun sa sun fita tun cikin kakar karshen karatu ta 2016/2017.
Wakilin mu ya kuma gano cewa mamacin, wanda har sakataren kungiyar bangaren da ya ke karatu ya yi a cikin 2016, ya sha wani abu mai guba ne ya mutu a shekaranjiya Lahadi.
Dama kuma cikin 2017 ne wata daliba a jami’ar mai suna Mercy Folaranmi, ta kashe kan ta saboda samun sakamakon jarabawa da bain yi mata kyau ba a daya daga cikin sauran darussan da ta ke yi.
Daga daga cikin ‘yan ajin su Olowoporoku mai suna Ayo Oyewole, ya shaida wa wakilin mu cewa abin ya firgita su matuka. Amma dai har yanzu fannin da mamacin ke karatu bai kai ga samun cikakken hakikanin yadda abin ya faru ba.
Sai dai kuma da PREMIUM TIMES ta tuntubi babban jami’in tsaron jami’ar, mai suna Babatunde Oyatokun, sai ya nuna bai san da labara ko bayanin rasuwar dalibin ba, wanda ya kashe kan sa.
“Ni ma a soshoyal midiya na karanta. Na ga an ce ya kashe kan sa saboda ya fadi wani kwas da ya kasa samun nasarar a kan sa. amma daga nan ban san komai a kai ba” Inji Oyetokun.
Wani abokin sa mai suna Moyiwa, ya ce tabbas mamacin ya na fama da darasi gda daya da ya hana shi fita daga Jami’a. Ni ma ina da wannan matsalar, amma dai ni na ci tawa jarabawar a bana.’’
“Su shida ne wadanda suka fita daga makarantar, amma ba su samu shaidar fita ba, saboda faduwa jarabawa da suka yi. Sun sake zauna jarabawar, amma daya daga cikin su ne kadai ya yi nasara.
“Na ji ana cewa za su je wurin malamin da ya kayar da su domin su roke shi. sannan kuma ya taba fada min cewa an takura masa a gidan su, su na so ya samu Sakamakon “First Class’’ ko “Second Class.”
Wakilin mu ya buga wa wani da ya je ta’aziyya wurin iyayen mamacin , inda suka nuna takaicin abin da ya faru. Sai dai kuma sun ce ba za su kara cewa komai ba, domin abin da ya faru dai ya riga ya faru.