Dakarun soji sun hallaka mahara 7 a Zamfara

0

A bayanan da rundunar sojin Najeriya ta aika wa PREMIUM TIMES, dakarun soji sun hallaka wasu mahara har su bakwai a wani samame da suka kai maboyar su.

Dakarun sun kai farmaki maboyan mahara da ke Aljumana Fulani da Ketere.

A wannan arangama da sukayi da maharan an kashe mahara 7 sannan wasu da dama sun arce da rauni a jikinsu.

Sannan kuma soja guda daya ya rasu a wannan arangama kuma wasu ‘yan banga da dama sun ji rauni.

Rundunar ta kara da cewa ta kama wasu masu aika wa maharan bayanan sirri dake zana tare da mutane a cikin gari.

Cikin su akwai wani da aka kama a wata kasuwa dake garin Shinkafi.

Anyi nasarar kwato bindigogi, harsasai da babura har bakwai sannan an fatattaka wuraren da suke buya da ajiye mutanen da suka yi garkuwa da a dazukan.

Share.

game da Author