Da sa hannun sarakunan gargajiya a rikice-rikicen Arewa – Ministan Tsaro

0

Ministan Tsaro, Mansur Dan Ali, ya yi ikirarin cewa akwai sa hannu da goyon bayan wasu sarakunan gargajiya a kashe-kashen da suka addabi kasar nan.

Ministan ya na magana ne a kan munin da hare-hare da garkuwa da mutane su ka haifar a Arewacin kasar nan.

Duk da dai bai ambaci sunayen su ba, amma ya ce lokaci ya kusa da za a fallasa su.

Dan Ali, wanda dan asalin Jihar Zamfara ne, ya ce sun samu bayanai da suka tabbatar da cewa akwai har da wasu manyan masu sarauta a ingiza fitintinu a Arewa.

Ya yi kira ga al’ummar karkara a jihohin da abin ya shafa da su goyi bayan gwamnati, wajen hada bayanan sirrin da za a bi a magance kashe-kashe a Arewa.

Ministan ya ce amfani da karfin soja kadai ba zai iya kawo karshen fitinar ba, sai an nemi goyon bayan jama’a.

“Yakin sunkuru da ta’addanci abu ne da suka buwayi duniya gaki daya. Don haka karfin soja kadai ba zai iya magance fitintinun ba.

Dan Ali ya ce an samu bayanai masu sahihanci cewa wasu sarakunan gargajiya kan bai wa mahara bayanai na sirri, har ma a kan samu masu fallasa shirin da soji kan yi.

Dan Ali bai fadi sunayen ko da basarake guda daya ba. Kuma bai ce jami’an tsaro sun kama kowa ba.

Share.

game da Author