CUWA-CUWA: An kori ‘yan sanda 9, an rage wa 6 mukami

0

Hukumar Kula Da Ladabtar Da ‘Yan Sanda Ta Kasa (PSC), ta kori wasu manyan jami’an ‘yan sanda 9.

Sannan kuma ta bada sanarwar rage wa wasu manyan jami’ai su shida mukami.

Hakan ya biyo bayan samun su da laifin tabka harkalla da cuwa-cuwa wajen daukar kuratan ‘yan sanda tun cikin 2011 da su ka yi.

Kakakin PSC, Ikechukwu Ani ne ya raba wa manema labarai wannan sanarwa a jiya Litinin, a Abuja.

Ani ya ce wadanda korar ta shafa tare kuma da gurfanar da su da za a yi a kotu, sun hada da: Abdul Yahaya Ahmed, Adamu Damji Abare, Osondu Christian, Pious Timiala, Agatha Usman da kuma Hassan Dass.

Wadanda aka rage wa girman mukamai kuma sun hada da: Oluwatoyin Adesupe, Mansir Bako, Gbenle Mathew, Tijjani Saifullah, Sadiq Idris da kuma Alice Abbah.

An yanke musu hukuncin kora da kuma rage mukaman a taron da Hukumar PSC ta gudanar na 5, a ranakun 26 da 27 Ga Maris, a Abuja.

Tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Musiliu Smith ne ya jagoranci taron.

Smith shi ne Shugaban Hukumar Kula Da Ladabtar Da ‘Yan Sanda Ta Kasa (PSC).

Share.

game da Author