CANJIN SHEKA: Kotu ta tsige sanatan da ya koma APC

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Abakaliki, babban birnin Jihar Ebonyi, ta tsige Sanata Sonni Ogbuoji, tare da umartar ya sauka daga mukamin da gaggawa.

A ranar Talata ne Mai Shari’a Akintola Aluko ya tsige shi saboda karya dokar Najeriya Sashe na 69(1)g na Kundin 1999 da ya yi, inda ya canja sheka daga wata jam’iyya zuwa wata, ba tare da dalili ba.

Shi dai wannan sashe na doka ya haramta wani ya fice daga jam’iyyar da aka zabe shi alhali ya na kan mukami ya koma wata jam’iyya, sai fa idan ana fama da rikici a jam’iyyar da ya ke ciki.

Har ila yau, kotu ta ce ya amayar da dukkan kudaden albashi, alawus da sauran kudaden da ya ci bayan ya canja sheka zuwa ranar da aka tsige shi.

Sannan kuma kotu ta umarci INEC ta kwace satifiket din san a cin zaben sanata, sannan ta sake sabon zaben sanata na shiyyar da ya fito.

A cikin hukuncin da Mai Shari’a Aluko ya yanke mai dauke da shafuka 71, ya ce Sanata Ogbuoji ya fice daga PDP zuwa APC a cikin 2018, ba tare da wani dalili ba.

Don haka mai shari’a ya ce ya karya doka da ka’idar ficewa daga jam’iyya zuwa wata wadda ba a karkashin ta aka zabi dan siyasa ba.

Wasu ‘yan takarar PDP ne suka kai kara cewa ya fice daga jam’iyyar su ba tare da akwai wata rigima a cikin jam’iyyar ta PDP ba.

Sannan sai suka nemi alkali ya tsige shi, domin PDP ce ta zabe shi ba APC ba.

Mai Shari’a ya gamsu da hujjojin cewa sanatan ya fice ne daga PDP salum-alum babu wata rigimar da ta yi dalilin ficewar sa.

Kokarin da ya yi na kare kan sa a kotu ya ci tura, domin a karshe kotu ta tabbatar da cewa wasu takardu da ya gabatar a kotun domin kafa hujjar ficewar ta sa, ba sahihai ba ne jabu ne.

Share.

game da Author