Shugba Muhammadu Buhari ya shirya tsaf domin barin Najeriya, zuwa kasar Ingila ziyara ta shi ta kan sa.
Fadar Shugaban Kasa ta bayyana haka a yau Alhamis da safe, cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai Femi Adesina ya sa wa hannu.
Buhari ya je Jihar Lagos jiya Laraba, inda ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar Lagos ta gina.
Sanarwar ta kara da cewa Buhari zai ziyarci Jihar Barno a yau Alhamis, domin bude wasu ayyuka da gwamnatin jihar ta aiwatar a fannonin ilmi, kiwon lafiya da titina, sannan ya zarce Ingila, inda zai shafe kwanaki 11 a can.
Ba a dai bayyana abin da zai je yi a Ingila ba.
“Bayan kammala ziyarar sa a Maiduguri, Shugaba Buhari zai zarce Birtaniya domin ziyara ta sa ta kan sa. ana sa ran dawowar sa a ranar 5 Ga Mayu, 2019.” Haka sanarwar ta bayyana, ba tare da karin bayanin abin da zai je yi ba.
Cikin makon jiya ne jaridar PUNCH ta buga labarin cewa a cikin shekaru hudu da Buhari yayi ya na mulki, ya shafe kwanaki 404 a kasashen waje.
Wadannan kwanaki sun haura kwanakin shekara daya kenan.
Idan ya tafi Ingila ya dawo bayan kwanaki 11 da aka ce zai yi a can, zai kasance ya yi kwanaki 415 kenan a kasashen waje daga cikin shekaru hudu da ya yi ya na mulki a zangon sa na farko.