Shugaba Muhammadu Buhari ya taya takwaran sa Firayi Minista Benjamin Netanyahu na Isra’ila murnar sake lashe zaben da aka gudanar a kasar Isra’ila.
Netanyahu zai ci gaba da zama Shugaban Isra’ila, bayan jam’iyyar su ta gamayya ta yi nasarar lashe zaben da aka gudanar.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Buhari, Garba Shehu ya sa wa hannu, ta ce “fatan alheri ga daukacin al’ummar kasar Isra’ila, bayan samun gagarimar nasarar kammala zabe. Ina yi musu fatan alheri, ina yi musu fatan samun zaman lafiya, ci gaba.”
“Shugaban Najeriya na son gani da fatan ci gaba da aiki kafada-da-kafada da Shugaban Isra’ila domin karfafa dankon zumuncin da ke tsakanin Najeriya da Isra’ila.
“Shugaba Buhari na yi wa Shugaba Netanyahu fatan samun nasarar a sabon zangon mulkin da zai kama, tare da addu’a cewa wannan zango na sa na biyar zai kawo zaman lafiya mai dorewa da samar da tsaro a Gabas ta Tsakiya.