Buhari ya daure ni bayan yayi wa Shagari juyin Mulki – Lamidon Adamawa

0

Lamidon Adamawa Mustapha Barkindo ya bayyana yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya daure shi a lokacin da yayi wa Shagari juyin mulki a 1983.

Lamido ya fadi haka ne da ya ke karbar bakuntar shuagaban kamfanin sadarwa, Watada communication Zubairu Idris a fadar sa.

” Dalilin da ya sa Buhari ya daure a wancan lokaci kuwa shine wai don na rike kujeran kwamishina a tsohuwar jihar Gongola, kuma a wannan lokaci Buhari ya umarci a kama duk wani wanda ya rike babban kujeran gwamnati a mulkin Shagari.

” Bayan an gudanar da bincike a ka samu ban saci kudin gwamnati ba, daga baya sai aka sake ni.

Lamido ya jinjina wa Buhari bisa Yaki da cin hanci da rashawa na gwamnati mai ci ke yi a kasar nan.

Share.

game da Author