Buhari ya bada umarnin gaggauta kai dauki ga yankunan da ake rikici a Adamawa da Taraba

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarnin a Gaggauta kai dauki a yankunan da rikicin kashe-kashe da kone-kone suka shafa a Jihar Adamawa da Taraba.

Shugaban Tawagar Kai Dauki, kuma Babban Daraktan Bincike da Ceton Rayuka na Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), Akube Iyawu, ya isa Yola.

Da ya ke bayani a Fadar Hamman Bata da Hamman Bachama a Demsa da Numan, ya ce sun je yankuman ne domin su tantance iayar asarar da aka yi ta rayuka da dukiyoyin jama’a a yankunan da rikice-rikicen suka yin kamari.

“ Shugaba Buhari kuma ya umarce mu da mu mika ta’aziyyar sa tare da kawo daukin agaji ga yankunan da abin ya shafa.”

Daga nan sai ya ce wadanda rikicin ya shafa su saurari isowar kayan agaji daga gwamnatin tarayya ta hannun Hukumar NEMA nan ba da dadewa ba.

A na su jawabai, Stephen Rmiya na Bachama da Alhamdu Teneke na Bata, sun nuna godiya ga Shugaban Kasa da har ya tuna da su a cikin wannan mawuyacin hali.

Sun kuma roki gwmnati da ta gano hanyoyin da za ta kawo karshen wadannan fitintinu a cikin yankunan al’ummar su.

Kauyuka guda biyu na Bolon da Barai ne a Jihar Adamawa suka fada cikin masifar mahara, inda suka kashe mutane shida, 10 kuma suka suka jikkata, duk a cikin Karamar Hukumar Demsa a Jihar Adamawa.

Masu tantance asarar sun ziyarci kauyukan Barai da Bolon da kuma Cocin LCCN da kuma Babban Asibitin Numan.

Share.

game da Author