A wani samame da Boko Haram su ka kai wa dakarun kasar Chadi, sun kashe sojoji bakwai sannan kuma suka jikkata 15.
Kakakin Dakarun Sojojin Chadi ya ce an kai harin ne a Kaiga Mindjiria, wani hari da ke Yankin Yammacin Chadi.
Azem Bermendoa Agouna ya bayyana haka jiya Litinin.
Su kuma sojojin sun yi ikirarin kashe Boko Haram su 63 a farmakin gefen Tabkin Chadi.
Kwanaki uku ne sojojin Najeriya suka bada sanarwar kashe Boko Haram da dama a farmakin hadin-guiwa da sojojin Chadi.