BINCIKE: An samu karuwa a yawan mutanen da suka kamu da cutar bakon dauro a duniya – WHO

0

Bisa ga binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta gudanar ya nuna cewa an sami karuwa a yawan mutanen dake kamuwa da cutar bakon dauro a duniya.

WHO ta gudanar da binciken ne daga 2016 zuwa 2018 sannan ta sanar da sakamakon binciken a shafinta na yanar gizo ranar Asabar.

Kungiyar kiwon lafiyar ta bayyana sakamakon binciken domin wayar da kan mutane mahimmancin yi wa yara allurar rigakafi musamman yadda duniya ke shirin shiga makon allurar rigakafi.

Sakamakon binciken ya nuna cewa a yankin Amurka mutane 12 ne suka kamu da cutar a 2016, a 2017 mutanen da suke kamu da cutar ya karu zuwa 775 daga nan a 2018 ya kai 16,689.

A kasashen Afrika kuwa mutane 36,269 ne suka kamu da cutar a 2016, a 2017 mutane 72,603 suka kamu da cutar sannan mutane 55,445 suka kamu da cutar a 2018.

Duk da haka binciken ya nuna cewa an sami raguwa a yawan mace macen mutane a duniya.

Binciken ya nuna cewa tallauci, yawan rikice-rikice, rashin bada hadin kai daga iyaye,rashin maida hankali wajen yin allurar rigakafi da wasu ma’aikatan kiwon lafiya da gwamnatocin kasashen yankin Afrika ke yi na daga cikin matsalolin da ake fama da su a kasashen Afrika.

Domin hana yaduwar cutar ne WHO ta hada kawance da kamfanin sarrafa magunguna GAVI domin samar da isassun alluran rigakafi musamman a irin kasashen dake fama da rashin zaman lafiya.

Cutar bakon dauro cuta ce dake yawan kama yara kanana musamman a lokacin yanayi na zafi.

Bincike ya nuna cewa kwayoyin cutar ‘Virus’ ne ke haddasa cutar sannan rashin daukan mataki game da cutar ne ke kawo ajalin yara.

Akan kamu da bakon dauro ta hanyar shakar kwayoyin wannan cuta a iska,yin tari,yawan zama da mai dauke da cutar,sannan cutar kan dauki tsawon kwanaki 14 kafin ya nuna alamu.

Alamun bakon dauro sun hada da zazzabi,tari,mura,kurarraji,rashin iya cin abinci da sauran su.

Malaman asibiti sun yi kira ga mutane da su hanzarta aka ga wadannan alamomi asibiti.

Yi wa yara allurar rigakafi a lokacin da ya kamata na cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutan.

Share.

game da Author